Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Qassam Reshen soji na Hamas, a ranar Asabar sun tabbatar da shahadar kwamandansu Izzud-Din al-Haddad a hukumance.
A cikin wata sanarwa da dakarun Al-Qassam suka fitar, an bayyana cewa Izzud-Din al-Haddad ya shahada tare da matarsa, 'yarsa, da wasu Falasdinawa da dama a wani harin Isra'ila. A cewar sanarwar, wannan harin an kai shi ne a tsakiyar birnin Gaza, wanda harin ke nuna "aikin ta'addanci na matsorata" daga abokan gaba.
Sanarwar ta kara da cewa wannan harin babban take yarjejeniyar tsagaita wuta ne. Al-Qassam ta kuma bayyana cewa za su ci gaba da jinjinawa shahidai, kuma gwagwarmayar Falasdinu ba za ta ja baya daga matsayinta ba.
Your Comment